MATAR DAMISA
(the wife of tiger)

Mallakin Asma’u Muhammad Auwal
ASMEETAH

NASARA WRITERS ASSOCIATION
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________

💫💫 *{{N W A}}* 💫💫

بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم

Book one 1.

Pages 1 to 10

Wata tsohuwar Mata ce zaune a bakin bishiya, ta jingina bayanta a jikin bishiyar tana shafa sumar kan Yarinyar dake kwance saman cinyarta,
Yarinyar bazata wuce 20yrs ba, tana kwance kamar mai yin bacci taji uwar tana shesshekar kuka! A firgice ta tashi zaune tana fadin “Uma lafiya kuwa, meya faru dake?”

Cikin kuka Tsohuwar tace “Ayush inaso ki tayani neman gafarar ubangiji, na tafka babban kuskure a rayuwata, inaji ajiki na zan mutu, Ayush! Zan mutu ba tareda na nemi yafiyar Junaid ba”
Lokaci guda ta fashe da matsanancin kuka mai kashe zuciya

“Uma Dan Allah ki daina kukan nan banso, banso na rinka ganinki acikin wannan halin,
Shin wanene wannan JUNAID din? Sannan mai kika Aikata masa haka har kike fad’in munanan kalamai akanki saboda shi? Cikin zubda hawaye Ayush take fad’in “Uma idan baki furta mun abunda ke ranki ba taya Zan iya temaka miki da Addu’a bayan bansan laifin da kika Aikata ba”
Cikin takaici da cije la66e Umma take kallon Ayush wacce itama Ayush d’in kallon Umman take,
“Ayush! Na tsani kaina, kema idan kika ji labarina na tabbata zaki tsaneni ne, Zan gaya miki Amma kafin nan inaso ki yafe mun Dan Allah” tana kallon Ayush cikin tausayawa.

Da mamaki a fuskar Ayush cikin kasalalliyar murya tace “ni kuma Uma? Nasan bakiyi mun komai ba, duk abinda kikayi mun nasan aciki soyayya ne, bazaki iya cutar dani ba Mamana, saboda haka na yafe miki duniya da lahira”. Murmushin takaici Umma tayi murya a sha’ke tace “Ayush a yanzu rayuwata batada amfani, a shirye nake dana mutu, sai dai Ina mai tausaya miki idan na mutu bansan halin da zaki shiga ba, Ayushh banida en uwa banida kowa, mutane gudu na suke saboda ban aikata abu mai kyau ba, hakan yasa laifi na ya shafeki kowa kyamar mu yake,” kinga can👉 ta nuna wani ‘Dakin Kara sannan ta cigaba da cewa “nasan kinsan cewa nan ne ‘Dakin mu na kwana, tin kina jaririya muke wannan dajin! Kinsha tambayata cewa Ina BABANKI, SU WAYE EN UWANKI amma na kasa baki amsarki saboda kada ki gujeni, amma yanzu a shirye nake dana fuskanci duk wani ‘Kalubale”

Taja dogon numfashi murya Ciki-ciki tace “AYUSH”
Cikin Sanyin murya ta amsa “Na’am Uma Ina sauraronki” fuskar nan duk ya jagalgale da hawaye ga yayi jawur abunka da farar mace.

Ta cigaba da cewa “Ina so naga kinyi Aure kin haihu, Ayush kina da kyakykyawar zuciya, kinada tausayi, Sam bana fatan ki d’auko kalar halina koda da qwayar zarrah, sannan banaso ki d’auko halin mahaifinki shima, tirrr da halayen mu” ta sake fashewa da wani sabon kukan mai cin rai!
Ayush itama kukan take ta rungumi Uma tana shafa bayanta rarrashinta take cikin kulawa, cikin sassanyar murya tace “Uma kibar mun wannan labarin indai zai Saki kuka, banson abunda zai sakaki kuka Umma nah Ina matukar kaunarki”

Umma ta raba jikinta dana Ayush tana sharar hawaye sannan tace ” a’a Ayush indai ban fitar da abunda ke raina ba, bazan samu nutsuwa ba,
Zan gaya miki ko ni wacece.

Da farko ni sunana *AGATHA* ni ba musulma bace, asalin er kasar Ghana ce ni, na rasa iyayena ta sanadiyar hatsarin motor, banida kowa bayan su saboda rashin zumuncin dake tsakaninsu da en uwansu hakan yasa basu ta6a gaya mun cewa inada en uwa ba, ni kuma ban damu da sanin hakan ba, ni dai nasan cewa mahaifina christal ne, mahaifiyata kuma musulma ce sai dai mahaifina ya rinjayeta zuwa chrital hakan yasa gava ta shiga tsakanin en uwan mahaifina da kuma mahaifiyata,
Sakamakon ba Wanda ya kula dani yasa na shiga harkar karuwanci ta hanyar nan nake ci da sha da kuma sutura a kaina,

Ina cikin wannan halin Allah ya had’ani da wani Attajirin Bawan Allah, ya fitar dani daga cikin wannan halin da nake ciki,

Ya taimake ni a rayuwa sannan ya kwad’aita mun musulunci, na musulunta ta sanadiyarsa, ya canza mun suna na koma *BARA’ATU* shi ‘Dan nan Nigeria ne kasuwanci ya kaishi kasar Ghana,
Nayi kusan shekara guda ina tare da shi amma ba wani abu daya ta6a shiga tsakanina dashi, nabi duk wasu hanyoyin dazan bi domin ya nemeni da lalata amma Sam yaki, ni kuma ina da munguwar sha’awa Gashi na kamu da matsanancin son sa,

Duk wani nauyi na akansa ya rataya shi yake mun komai hatta kudin da zan kashe shi yake ban,
Wata rana yana zaune yanata Lissafe-lissafensa na kudurta a raina cewa zan sanar masa cewa ina sonsa kuma zan Aure shi,
Bayan na sanar masa bai nuna mun 6acin ransa ba amma sai dai yaki amincewa da Aurena,
Kinsan mai ya cemun??

Ta karasa maganar tareda tambayar Ayush.
Girgiza Kai Ayush tayi tareda ‘kura Mata ido cikeda mamaki take kallon mahaifiyar tatan,
Ta cigaba da cewa “naji takaicin maganar daya gaya mun”
Hmmmm! Taja ajiyar zuciya sannan tace “cewa yayi yabar Matarsa a Nigeria tare da ‘Dansa, baya bukatar ‘Kara Aure saboda gudun matsala!

Sannan yace “zai tafi Dani gidansa a matsayin er Aikin matarsa,”
Ayush zaro Manya-manyan idanuwanta tayi waje tana kallon mahaifiyar ta, ta rasa abun cewa
Sai ji tayi Umma tace “a lokacin na kudurta a raina cewa saina rabashi da matarsa, saboda Ina matukar kishinsa, kuma sai nabi ta hanyar dazan bi na Aure shi,
Na bishi a hakan har muka komo Nigeria, ya gabatar dani a wajen matarsa Doctor Fateemah mutumiyar kirki, batada tashin hankali, sai ‘Dansa mai suna Junaid karamin yaro ne lokacin baifi 10yrs ba,

Alhajin bai 6oyewa matarsa komai ba ta yanda muka hadu, sai dai bai sanar mata da cewa ina sonsa ba,
Na fara gabatar da Aikin gidan a matsayin er Aiki suna biyana salary duk wata”
Umma ta dakatar da labarin tayi shuru kamar mai tunanin wani abu sannan tasau murmushin takaici

Ta cigaba da cewa “a lokacin na nemi wani hatsabibin boka babban matsafin duniya, ta hanya wata shu’umar mata wacce muka hada kawance da ita,
Tafiya mai nisa mukayi domin zuwa gurin bokan ni da kawata,
Kuma mun sameshi amma guri ne mai hatsarin gaske ba kowa ne yake zuwa dajin ba sai mai karfin ikoh,
Na sameshi da maganar Alhajin nan, Bokan yayi wani irin matsanancin Dariya mai rikitarwa sannan ya sanar mun cewa
Zan mallaka masa Abu uku ne kafin ya biya mun bukatata,
Na farko zan bashi kudi 100Bs,
Na biyu zan mallaka masa jinin yaro namiji domin biyan bukatarsa na daban ,

Na uku zan bashi kaina, ma’ana yayi lalata Dani,
Duk na amince masa saboda nima inason bukatata ta biya,
Sai dai Abu na farkon daya fad’a shine zai ban wahalar samu wato 100Bs,
Bayan mun bar dajin hotel muka Kama saboda garin yayi nisa sosai,
Anan ne nayi shawara da kawartawan akan batun kudin
Ta sanar mun cewa wannan bazaiyi wahalar samu ba, nayi mamakin jin hakan saboda kudi ne mai yawan gaske,

Daga baya tace mun zata iya bani duk kudin kyauta amma saina bata Abu daya,
Na nuna Mata cewa komai ma zan iya bata indai zan samu kudin,
Ashe cikakkiyar er lesbian ce (madigo)
Ban nuna Mata komai ba sai cewa nayi na Amince “na mallakawa ‘katon boka mah balle ke kawata”

Taji dadin wannan furucin nawa
Haka muka aikata madigo cikin jin dadin juna ba tareda fargaban komai ba, ta mallaka mun kudaden nan nakaiwa boka, shima na bashi abunda yake bukata ajikina sannan na bashi yaron Alhaji wato Junaid,

Sai dai kash abun bakin ciki anan shine Bokon nan yana son haihuwa amma manyan Aljanunsa sun hanashi har saiya mallaka musu jinin yaro namiji kafin su bashi haihuwar,
Ya nemi Mata da yawa amma ba haihuwar, yaran da suke kawo masa jininsu baiyi dai dai da kalar jinin da suke nema ba shiyasa ya hakura da neman matan,
Sai akaina kuma jinin Junaid yazo dai dai da jinin da suke bukata,

Boka yayi matukar farin ciki sosai, ya kamu da sona hakan yasa ya ruguje duk wani tsafin da yayi don na mallaki alhaji, yace “bazan Auri kowa ba, kuma bazai Aureni ba saboda su basa Aure,
Bansan hakan ba sai da ciki ya fara 6illowa daga tumbina, na tsorita sosai,

Har cikin ya girma! shi kuma bokan ya haskaka madubinsa gareni duk wani motsina yana gani ta madubi, kuma duk abunda nakeso zai bani saboda cikin dake jikina,
Har Allah yasa na haihu jaririyar mace ba kowa bace face ke *AYUSHMAT*
Ayush suman zaune tayi jin mahaifiyarta ta ambaci ita diyar boka ce
Innalillahi wa inna’ilaihi raju’un,

Abunda Ayush taketa furtawa kenam,
“Umma kin cuceni, kin ‘kazantar mun da rayuwata, na shiga uku nah, wayyo Allah nah, Umma laifinki babba ne, kin gama da rayuwata, bayan ni er cikin shege ce hakan mah diyar babban boka iblis”

Cikin takaici ta zubawa mahaifiyarta ido, idanunta duk sunyi jaa tsabar zubar hawaye, ta lankwasa wuya ta zamo kalar tausayi, murya a sanyaye take fad’in “Umma ya rayuwarki a haka? Meyasa kika za6arwa kanki kalar ‘kazamar rayuwar nan , Gashi nima ya shafeni, Allah sarki Junaid yaro bai san komai ba gashi an jefa rayuwarsa cikin hatsari”

Umma Bara’atu gaba daya ta susuce, ta fita hayyacin ta, idanuwanta duk sun ‘kan’kance tsabar kuka, bakinta na rawa tace “Ayush kiyi hakuri, nasan na cutar da rayuwarki, naso ace kema kin zamo d’iya mai enci” kuka ne yazo mata mai cin rai.

Cikin tausayawa Ayush ta kamo hannun Uman tana rarrashinta “Umma ki daina kukan nan, ki sanar mun abunda ya faru bayan nan”
Umma ta d’ago da rinanan idanuwanta tana kallon Ayush wanda itama kukan take ta gagara rarrashin kanta domin abun da ciwo,

Cikin karayar murya Umma tace “Ayush! Bayan na haifeki na nuna cewa ke d’iyar Alhaji ce, wanda hakan ya jawo rashin jituwa tsakaninsa da matarsa, nasa Alhaji kuka cirr da idanunsa yana rantsuwa akan shi bai ta6a kusantar zina ba, baisan ya akayi na samu cikinki ba, naji tausayinsa alokacin sai dai inaso ya amince da ke a matsayin d’iyarsa” bata karisa maganar ba taji Ayush ta katseta da cewa “tayaya Umma, taya zai yadda ni diyarsa ce bayan yasan ba alakar data shiga tsakanin ku, haba Umma”

Cikin kuka Umma tace “toh ki tsaya mana ki saurareni, ai a lokacin matarsa cewa tayi bazata cigaba da zama dashi ba, naji dadin hakan sosai saboda nasan ko bai Aureni ba zamuyi zaman dadiro ne da shi, Amma sai dai kash yana cikin bawa matarsa hakuri zuciyarsa ta buga lokaci guda Alhaji ya rasa rayuwarsa,

Innalillahi wa inna ilaihi raju’un Allah sarki Alhaji ka gafarce ni” ta Kara fashewa da wani irin kuka,
Ta cigaba da cewa bayan rasuwar Alhaji an gano cewa karya nake Anyi mun korar kare a gidan nan, har hukuma sai da ta kulleni daga baya mahaifinki yazo ya yi baili na,
Mutane sun kyamaceni, wasu har tofa mun yawu suke da zaran nazo wuce wa, gaba daya zaman cikin garin ya gagareni hakan yasa mukazo nan dajin da zama,

Na kuma yanke alakata da mahaifinki babu ni babu shi amma duk da hakan bai daina bibiyata ba saboda ke, yanzu haka yana kallon mu ta cikin madubinsa kuma yana jin duk abunda nake fad’a,
Rauninsa kuma kece”
Wani irin juya ido Ayush tayi tana wani yamutsa fuska kamar mai jin kyama tace “ni kuma? Tayaya rauninsa zai zama daga gareni yake, can’t believe”

Murmushi Umma tayi sannan tace “kwarai kuwa, duk wani abun cutarwar da zai sameki to shima haka, idan kika ji ciwo a jikinki toh shima zaiji zafin ciwon a jikinsa, shiyasa tin kina karama idan kikayi laifi bana dukanki saboda zai d’au fansa ne domin shi zaiji zafin dukan, idan kikayi zazza6i toh shima a ranar zai kwanta jinya, duk abunda ya faru da ke shima zai faru da shi, sai dai kuma shi ata 6angarensa duk abunda ya faru dashi babu abunda zakiji”

Ayush ido ta zaro waje still tayi tambaya atakaice “Umma duk meya jawo hakan?”
“Saboda rauninsa yana daga gareki ne, akwai abunda ya ajiye a jikinki wanda shine rauninsa, da zarar kin cire wannan abun toh duk wani tsafinsa zai lalace, duk wani sihirinsa zai karye, kuma daga karshe zai iya rasa rayuwarsa”

A firgice Ayush tace “Umma meye abun dake jikina? Inason saninsa”
Numfashi Sama-sama Umma take jaa saboda ba karamin azabtar da ita bokan nan yake ba domin tanaso ta fad’awa d’iyarsa sirrinsa wanda ba kowane ya sani ba,
Ta cikin madubin yake watsa mata tafashashshen ruwan zafi, duk jikinta yayi jawur ita kadai tasan irin rad’ad’in da takeji, amma ita Ayush bata san da hakan ba, ta zubawa mahaifiyar ta ido tana kallon ikon Allah “shin meyasa Umma taketa yunkurawa ne kamar wacce jikinta ke Mata kyaikayi”
Muryar Umma na rawa take fad’in “Zan gaya miki wani Abu Ayush ko zan mutu,

Junaid yana cikin mawuyancin hali, sun bada jininsa a wani tsohon DAMUSAN SU wanda yake bukatar jinin yaro, Damusan yana taimaka musu waran tsafinsu, kuma zai iya mutuwa indai ba’a bashi jini yasha ba, jinin mah sai wanda ya za6a bazai sha jinin kowa ba sai wanda ya burge shi, ankai mishi jinin yara da yawa amma ya’ki shan jinin kowa, duk jinin da bai sha ba yaron mutuwa yake, anyi asarar rayukan yara maza da dama, sai da aka kawo masa jinin *JUNAID* kafin Damusan nan yasha, atake Damusan ya samu lafiya ya mi’ke, jinin Junaid yana gudana ne a jikin Damusan,
Shiyasa da zaran ran Damusan ya 6aci shikenam za’a nemi hankalin Junaid a rasa”,
Tashin Hankali ya Junaid zai kasance???

Labari Umma take badawa!
“Tin lokacin da Damusa yasha jinin Junaid daga lokacin Junaid ya zamo ‘Karfafan Namiji, yanzu shekarunsa 30 cif Amma bai San sha’awa ba, ko kallon mace bayayi balle yaji sonta a ransa, sun gusar masa da duk wani tunaninsa,
Idan ran Junaid ya 6aci to kowa ya shiga uku, domin zai iyayin kisan Kai ba tareda saninsa ba,
Zai zamana duk wani ire-ire na Damusa zai rinka yinsa hatta kalar kukan Damusa zai rinka yinsa tareda gurnani kalar na namun daji,

Idanunsa zasu koma irin na Damusa, kukansa irin na Damusa, sannan ko wani lokaci zai rinka jin kamshin mutum, ga ‘karfi ba’a magana duk da saninsa danayi yana yaro ‘karfin bala’i gare shi, ya ‘Karfinsa zai kasance yanzu kuma? Hakan yasa bashida Aboki ko d’aya, daga shi sai mahaifiyarsa ita ke kula dashi, duk da kudin da suke dashi nasan bata cikin kwanciyar hankali, malumai da dama sun kasa ceton Junaid a halinda yake ciki,
Junaid yana zama cikin hankalisa amma duk sanda Damusan ya motsa masa tofa ba zaman lafiya, kowa tsere mishi yake sai dai idan anyi gaggawar d’aureshi da igiya mai karfin gaske,”
Umma tana zubda hawaye tana fad’in “ni dai nasan Damusan bazai bar jikin Junaid ba, duk sanda Damusan nan ya mutu shikenam shima Junaid mutuwa zaiyi”

Ayush kam tayi sumar zaune idon ta ya ‘kame ‘kam ko ‘kifta su batayi,
Umma ce ta bubbuge kafad’arta sannan tayi firgitt ta dawo daga sumar zaunen,
Tsananin tsorone ya bayyana a fuskar Ayush jin yanayin da Junaid ke ciki duk da bata sanshi ba amma tana jin fargabar haduwa da shi “hatta idanunsa komawa yake irin na Damusa?”. Tayi tambayar a ranta tareda jinjina kai ,
Ayush ce ta maido hankalinta kan mahaifiyarta sannan tace “Umma kenam bashida magani shi ciwon Junaid din?”
Wani irin murmushi Umma tayi mai ‘kona rai sannan tace “akwai mana, warakar ciwon Junaid yana a jikin ki”
Wani irin had’iyar yawu Ayush tayi ido waje tace “Umma meyasa duk wani tsafinsu yake jikina, shin meye abun dake jikina?”

Tace “ba nace miki raunin mahaifinki yana jikinki ba, to haka shima Damusan tsafinsa yana jikin mahaifinki, da zarar kin cire wannan abun dake jikinki shikenam kin lalata komai, kin tarwatsa mahaifinki sannan kuma Damusan shima tsafinsa zai lalace da zaran tsafin Damusan ya lalace kuma shikenam Junaid zai samu lafiya, Damusan zai fita daga jikinsa,
Sai dai hakan zaiyi matukar wahala saboda dole saikin zubda jininki sosai kafin abun ya fita daga jikinki hakan kuma zai iya jawowa ki rasa rayuwarki”

Fashewa Ayush tayi da kukan gaske tana fad’in “Umma ki gaya mun abunda ke jikina, wallahi nayi Alkawari ko zan rasa rayuwata saina tarwatsa tsafin mahaifina sannan na ceto rayuwar Junaid” kuka takeyi sosai.
Cikin lallami Umma take fad’in “Zan gaya miki Ayush, badon zaki raunana ba dana dad’e da cire miki saidai mahaifinki bazai bari hakan ta faru ba, saboda hatsabibin boka ne,
Amma Zan gaya miki kodan saboda rayuwar Junaid”,
Tana zubda hawaye tace ” *AYUSHMAT* wannan abun tsafin ba komai bane face abunda ke jikin!!
Bata ‘karasa maganar ba taji an sha’ko mata ma’kogaro, numfashi Sama-sama Umma take ta zaro ido waje,

Ji tayi daga sama ana magana cikin tsawa ” KEE BARA’ATU NI ZAKI CIWA AMANA A GABAN ‘DIYATA ZAKI TONA MUN ASIRI, ZAKI MUTU! ZAKI MUTU!! ZAKI MUTU!!! HAHAHA, HAHAHAHA,
Dariya ne mai rikitarwa, nan take ta rasa hankalin ta,
Itama dariyar ta farayi, tana tafa hannayen ta biyu tare da fad’in ” *Junaid* *Damusa* *wayyo* *Damusa* *kamoshi* *naan*” haka ta rinka Maimaitawa tana kwashewa da dariya, alamu sun nuna cewa Uma ta haukace.

Salati Ayush ta shiga yi tana fad’in “Uma meye haka? Dan Allah ki daina” kuka ne yaci raanta sosai, tazo zata rungumi mahaifiyar tatan. A haukace Uma ta cillata gefe guda tana fad’in “Damusa ce ke! Kar ki ta6ani, Damusa ce ke!! Ta tashi da gudun gaske ta nufi bakin hanya.
Itama Ayush binta tayi tana kuka tana fad’in “Umma Ina zaki je ki dawo dan Allah!.. Kafin Ayush ta sake magana wata karamar motor ce ‘kirar Jeep brown colour ta taho da gudun gaske bata Ankara ba tayi sama da Umma, kanta ne yayi mungun buguwa a saman kwalta , kafin kace mai jini kamar anbaliya,

Innalillahi wa inna’ilaihi raju’un daman Umma mutuwa take jira Gashi kuwa rai yayi halinsa, sai ido a bud’e.
Wani irin ‘Kara Ayush tayi mai rikitarwa, da gudun gaske ta nufi Uman wacce take kwance …

Tsugunawa Ayush tayi gaban Uma tana girgiza ta ” Dan Allah Uma ki tashi karki mutu ki barni, Idan kika mutu ban San ina zansa kaina baaa” wani irin kuka take na fitar hankali “wayyo Umanaa, ki tashi mana”

Duk kukan da take mai motar yana kallonta ta cikin madubin motarsa ko fitowa bai samu damar yiba,
Motarsa ya fara ja a hankali zai bar wajen!
Cikin 6acin rai Ayush ta mi’ke ta d’auki wani qaton dutsi ta wurga bayan motor da shi, nan take glass d’in motor ta fashe, kansa ne ya bugu da sitiarin motar tsabar burkin daya Danna,

Ransa ne yayi matukar 6aci, DA karfin gaske ya cankar da marfin motar da kafarsa ya fito yana huci.

Itama Ayush gabansa tazo tana fad’in “Kai wani irin Dabban mutum ne Wanda baka San darajan Dan Adam ba, mungu, Azzalumi Mahaifiyata ka buge amma kamar Wanda ka kashe kiyashi,”
Ya kasa juran kalamanta haka yasa hannu ya shaqo wuyanta da karfin gaske, ya d’agata sama da hannu daya, idanuwansa ne suka fara chanza colour,
Ta tsorita sosai da ganin shi haka, ido ta zaro waje tana kakakin mutuwa,
Wani irin shocking yaji yabi jikinsa kamar Wanda ya rungumi electric gass, jiyayi kamar wuta ne yake ci a jikinsa,

Da ‘kyarr ya iya wurgar da ita gefe, sauran kad’an ya fad’i ‘kasi badon ya ri’ke motarsa da karfi ba, a gigice ya shige cikin motarsa ya figeta da gudun gaske! Shi kad’ai yasan irin rad’ad’in da yake ji a jikinsa, ga hankalinsa ya fara barin jikinsa.

Ayush tashi tayi tangal tangal kamar zata wad’i kasi tayi gurin da mahaifiyar take kwance ta fad’a saman ta, numfashin ta ne ya tsaya cakk, lokaci guda ta sume a gurin.

Motar ce tasau hanya sakamakon ba’a cikin hayyacinsa yake ba, cikin jeji motar ta gangara wata ‘katuwar bishiya motar ta daka, kansa ne yayi wani irin buguwa a take shima ya suma………

 

 

FAST DOWNLOAD

DOWNLOAD COMPLETE PDF HERE

How To Get Complete Matar Damisa Book 1

The most reliable and easiest way to obtain the completeMatar Damisa Book 1 isto purchase them from Jambandwaec.com (JAW) Novel Store, because we remain the best in delivering the true novels you will definitely enjoy.

You can get the complete Matar Damisa Book 1 in Portable Document Format (PDF) for just ₦1,000.

JAW remains the best, reliable and most credible resources you will find online as it is also well Arranged in PDF.

To get your own copy of the completeMatar Damisa Book 1booklet, follow these simple steps:

Step 1: Visit the DOWNLOAD LINK to make a payment.

Step 2: Fill in the form with the right information including emails, and title of novel.

Step 3: Make payment for the booklet using your preferred payment method.

Step 4: Once payment is confirmed, you will receive an email containing the PDF of the novel you want.

DOWNLOAD COMPLETE PDF HERE

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Explore More

Download Complete MATAR DAMUSA by MALLAKIN ASMEETAH Romantic Hausa Novel PDF

February 14, 2024 0 Comments 0 tags

FREE BOOK MATAR DAMUSA (the wife of tiger) MALLAKIN ASMEETAH NASARA WRITERS ASSOCIATION ___________________________________ {{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }} ___________________________________ *{{N

Download Complete Yar Aikin Karuwai Book 2 Page 111-115 Hausa Novel PDF

February 14, 2024 0 Comments 0 tags

YAR AIKIN KARUWAI 2 🌼 MATAFIYA BOOK 2 111-115 Official By AsmaBaffa SADAUKARWA GA ZAINAB USMAN GARKUWAR MATA *Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk

Dowload Budurcina Yancina by Benaxir Omar Hausa Novel Complete PDF

February 14, 2024 0 Comments 0 tags

BUDURCINA YANCINA NA BENAXIR OMAR Sunana Ambar,Rayuwata tana cike da darasi,tausayi,alajabi, haushi dakuma dana sani, bana kaunar kowacce ya mace ta kasance acikin halin dana shiga koda kuwa makiyata ne,