ABBAN SOJOJI

The Father Of Soldiers
Na
Hafsat Bature Moh’d
~BossLady~
🔔🔔🔔

Page 94-95

a hankali ta buɗe kopan ta fito cikin sanɗa, gabanta ne ya faɗi da ta hango su gaba ɗaya sun hallara a babban palorn cikin tashin hankalin rashin junaid, har sun fara yanke sha’warar fara kiran friends ɗinsa da sauran ƴan uwa aji koya je can,
Dafe zuciya sehrish tayi tabbas kuwa in tabi ta entry ɗin main palor zasu tambaye ta jin ba’asin ina xataje, don haka tayi deciding ta canza hanya cos there’s many doors acikin gidan da zaka iya fita compound ɗin gidan,
Ja da baya tayi a hankali dama slippers ne a ƙafarta marasa sauti, cikin sanɗa ta lallaba, ta miƙi doguwar hanyar da zata sada ta da backyard ɗin gidan,
Taci sa’a akwai Key ajikin ƙopan jikinta na kerma tasanya hannu ta murɗa key ɗin kopan ta buɗe, ahankali ta zura ƙafa ta fuce,
tsoranta kada security guard ɗin dake strolling acikin gidan su ganta a daren nan tana shawagi tabbas sai sun tuhume ta, gashi ko’ina na gidan Haske ne 6ayau kamar rana saboda fitilun kwan da aka ƙawata shi dasu masu hasken da kyan gaske kamar rana,
A hankali sehrish ke tafiya kamar 6arauniya, har Allah ya shigar da ita cikin garden ɗin kai tsaye wurin da garden chairs ɗin suke ta tunkara,
tunkan ta ƙarasa ta Hango mutun a ƙanƙame saman kujera ya kifa kansa saman table ɗin gabansa, gaba ɗaya jikinsa sai kermar sanyi yake na tashin hankali,
Zaro ido sehrish tayi cikin tsananin tashin hankali ta watsa aguje inda yake gabanta na faɗuwa, tabbas kuwa Junaid ne, dafe kanta tayi tare da cewa “Innalallahi wa’inna ilaihirraji’un !!! Nashiga Ukuna ! Junaid meyasa !!!!!
Cikin tashin hankali tayi maganar tuni hawaye sunzo mata shar a face ɗinta,
Matsawa tayi dab dashi tasa hannu ta bubbuga table ɗin dake gabansa murya a mace take ambaton sunan shi “Junaid…junaid…,’
Wani irin dogon numfashi yaja hatta yatsun hannayansa kerma suke yi, ko eyes ɗinsa bai iya buɗewa tabbas yaji Muryar sehrish amma sam yagaza bata amsa, so yake yayi mata magana taje ta sanar da wani daga cikin gidan yazo ya taimaka mishi ya tashi amma ya gaza, saboda sautin muryarsa baya fita, Lips ɗin ma nasa rawa suke yi kaf kaf,
Bin ziraran yatsun hannun shi tayi da kallo ganin suna kerma kaf ! kaf !! Hakan ya tabbatar mata da cewa Junaid idonshi biyu, sanyi ne yakamashi ssae,.
Cikin sauri sehrish ta cire mayafin da take naɗe gashin kanta dashi ta rufa ma junaid abayansa, duk da mayafin bai da wani kaurin da zai masa magani,
Zubewa tayi saman guiwarta agaban table ɗin, saitin fuskarshi dake kwance saman table ɗin tace “Junaid meyasa? Why pls? meyasa zaka cutar da kanka har haka? dan Allah ka buɗe idonka junaid, ka tashi mu tafi,’
Daker numfashinsa ke fita sam sehrish batayi tunanin tana 6ata lokaci ba wurin agaza masa,
So yake ya buɗe idonsa ya kalle ta amma sam ya gaza, sai kerma eye lids ɗinsa suke yi,
Hawaye ne kawae ke fita a idon Reesh, tana cikin wannan zuƙunnan karaf idonta suka sauka akan Hancinsa da Jini ke ɗigo wa,
Waro ido tayi waje a firgice ta fashe da kuka tare da faɗin “Junaidd…!!! innalallahi wa’inna ilaihirraji’un nashiga ukuna Wayyo Allah !!!
A zabure ta miƙe ta juya da gudu don taje ta sanarwa Aunty azmee wata’ƙil ta taimaka wurin sanar dasu halin da Romeo yake ciki don azo ataimake shi karya mutu,
Har Tayi nisa da gudun nata muryar shi ta ratsa kunnan ta “Sehrishhhhhhhh,” cikin wata irin matacciyar murya wadda ta galabaita yyi maganar,
A razane ta dakata tare da juyo tana kallon shi, samun shi tayi ya buɗe idonshi waɗanda suka rune jawur daker yake ƴunƙurin tayar da jikinsa da dukkan sauran ƙarfinsa,
Cikin tsananin tausayi sehrish ta koma da gudu wurinsa tana faɗin “junaid,’ tashi yayi zaune yana fidda numfashi a hargitse muryarsa na rawa yace “ki taimaka mun numfashi na zai iya ɗauke wa, ki goyani ki kaini wurin Abbana,’
ɗan zaro ido tayi tana kallonsa can kuma tayi tunanin ae junaid bazaiyi nauyi ba, ba wani girman jiki gare shi ba, duka nawa yake
daddagewa sehrish tayi ta tsugunna masa tare da cewa “hau muje,” daker junaid ya sauko ya faɗo bayanta tare da ƙanƙameta yana numfashi a sama sama,
Jigumm sehrish tayi saboda wani abu da taji ya yi mata yawo ajikinta,
“Ki tashi mana so kike na mutu ko,” junaid ne yayi maganar daker cikin shagwa6a, bawan Allah,
Da iya ƙarfinta na ƙarshe, daker sehrish ta miƙe tana tangal tangal zata faɗi amma ta hana hakan, ta dake ta cije ta miƙi hanyar fita daga garden ɗin da junaid goye abayanta kamar wani ƙaramin yaro, ya lafe abayan sehrish ɗinsa, tana jin numfashinsa a gefen wuyanta saboda nan hancinsa yake, tana jin yarda junaid ya ƙanƙame mata stomach ɗinta saboda ta nan ya zagayo da hannayensa,
Cikin sa’a ta fuce dashi daga garden ɗin kuma ba wanda ya ganta har ta shige dashi cikin ƙopan da ta fito, yanzu tunaninta shine yarda za’ae ta haɗa junaid da ƴan uwansa batare da wani ya ganta ba, tsayawa tayi tana wannan tunanin aikuwa junaid ya fashe mata da kuka mai sautin gaske yana cewa “wai bazaki shiga dani ba so kike na mutu ko,’ duk yarda sehrish taso ta hana junaid magana abun ya faskara sai ma ya ƙara sautin kukan wanda hakan ya janyo hankalin Mutanen gidan dake a falo,
. gaba ɗayansu sunji kukan junaid da muryarsa, har haɗa baki suke yi wurin cewa “Kai wannan ae kukan junaid ne !!,’
gaba ɗayansu suka nufi hanyar da suka jiyo muryar junaid yana kuka yana yima sehrish faɗa akan taƙi ta motsa takai shi ɗakinsu,
Jin takon takalmansu alaman sun tunkaro wurin yasa sehrish shiga tashin hankalin, gashi ta cire mayafinta, hular kanta ta karkace dogon gashin kanta duk ya barbazo waje, ae kuwa a firgice ta saki Junaid ya faɗi ƙasa tumm !tayi saurin zame mayafinta dake jikinsa, kamar aljana tayi Wuff ta boye a wani saƙo hannunta dafe da saitin zuciyarta,
Junaid kuwa ganin sehrish ta jefar dashi ƙasa ta gudu yasa shi ƙara sautin kukan nashi ya karaɗe ko’ina yadinga burgima a ƙasa yana faɗin “wayyo Allah na, ta jefar ni !! bazaki zo ki goyani ba ki maida ni wurin Abbana ba, Wlh saina tona miki asiri tunda kikai mun hakan…….’ sam junaid fa baya cikin hayyacinsa yake waɗannan maganganun, sehrish kuwa saboda ruɗin abunda junaid yace, tuni futsari ya kufce mata ta cikin wandonta ya soma zuba zirrrrrrrrrr ! Mai zafin gaske cije le6enta tayi tare da runtse idanunta,
Isowa su kayi gaba ɗayansu sunyi mamakin ganin junaid baje a ƙasa yana burgima sai faman sambatu yakeyi yana faɗin “wlh saina tona miki asiri kowa ma yasani Allah,’ cikin kuka da shagwa6a yake maganar,
Atare suka haɗa baki suna cewa “Junaid ! ina ka shiga muna ta nemanka? Kai da wanene ? Ta ina ka shigo,’
Jin muryoyinsu yasa shi dakatawa yana kallonsu idonshi biji biji sam bai gane su wanene akanshi,
Murya na kerma yace “ita ce ta shigo dani, ta goyani kuma ta jefar dani ƙasa ta boye acan wurin,’ yayi maganar yana nuna inda sehrish ta 6oye,
Tuni temperature ɗin jikin sehrish ya ɗau wani irin mahaukacin zafi, nan take wani futsarin ya sake zubo mata na tashin hankali, tuni zufa ta gama wanko mata sharkaf wandon jikinta kuwa ya jiƙe sharr,
Babu abunda take furtawa Acikin zuciyarta fa ce “La’ila ha illah anta subhanaka inni kuntu minal Zalimin,’
Gaba ɗaya idonsu ya kai inda junaid ya nuna musu,
“Ah Wannan Fa aikin shaiɗanun aljanu ne kubarmin kawai A ya neh nayi maganin ƴan Iskan,” acewar haroon
Yana maganar ya nufin wurin,
Sgr bai tsaya jin bayanansu ba, hannu kawai yasa ya ɗago junaid dake kwance, ya ɗauke sa kamar wani ƙaramin yaro ya aza shi a ƙafaɗarsa, ya juya batare da ce musu komai ba ya wuce dashi part ɗinsa,
Shi dae abbansu ajiyar zuciya kawai yake saki tunda Allah ya dawo masa da Baby junaid ɗinsa lafiya, kallon sauran yayi tare da cewa “Kowa yaje ya kwanta, koma mekenan gobe zamu duba,”
Juyawa su kayi gaba ɗayansu kowa na faman sauke ajiyar zuciya suka wuce rooms ɗinsu, ban da haroon wanda ke faman sakin murmushin mugunta, domin kuwa ya hango ƙafafun sehrish masu sanye da wannan slippers ɗin nata na ƴan gado,
Bayan kowa ya bar wurin, sehrish tayi tunanin ta lalla6a ta wuce ɗakinta, dama idonta na runtse a hankali ta buɗesu gaf taga fuskar haroon a kusa da tata, wage baki tayi zatayi Ihu yayi saurin sanya hannunsa ya toshe mata baki yana faɗin “Ƴar shila, ae dama nasan kece ja’ira, na hango waɗan nan ƙafafuwan naki masu kama dana Zabbi,’
Tsananin bakin ciki ne ya cika sehrish ganin mutumin da ta tsana,
A faɗace tasanya hannunta tare da Buge nasa, da gudun gaske ta wuce shi ta faɗa bedroom ɗinta tana shessheƙar kuka, datse ƙopan tayi gudun kada haroon yasamu damar faɗo mata,
Jingina jikinta tayi jikin ƙopan bayan ta rufe, tana kuka mai cin rai, ta ƙara jin tsanar haroon a ranta hada shine yaja mata barin junaid yayi ta faman jiran ta a garden gashi hakan yayi masa Illah ssae, duk inta tuna ɗigon jinin junaid da tagani daga hancinsa, sai taji wani irin ba daɗi aranta,
Ta jima jikin kopan kafin daga bisani ta wuce toilet ta tu6e wandon daya jiƙe sharkaf da futsari tasa shi a bucket ta wanke sa, sannan ta shanya shi a siririyar rigiyar dake a toilet ɗin, wadda akayi ta domin shanya panties, da hanging ɗin kaya, bayan ta kammala tayo wanka sannan ta fito ta canza wasu kayan riga da wando
daga bisani ta haye saman gadonta tana sauke ajiyar zuciya, shigewa tayi cikin bargo tana dariya lokaci guda da ta tuna abunda junaid yaso yayi mata a yau da ta shiga uku kuwa, daker bacci 6arawo yayi awon gaba da ita,
A hankali Babban yaya ya kwantar da junaid saman shimfiɗeɗan gadonsa, har lokacin junaid fa bai dae na sambatu ba akan abunda sehrish tayi masa, sai da yaji yatsun sgr a bakinsa, sannan ya ware idonsa da kyau yana kallonsa, yayi tsit daga maganar da yake yi,
Tashi yayi ya kashe a.c ɗin ɗakin gaba ɗaya, sannan ya kunna masa Room heater (na’urar dake ɗumama ɗaki ta zafi) nan take bedroom ɗin ya ɗumama da wani irin ɗumi mai daɗin gaske, hakan yasanya junaid fara dawowa cikin hayyacinsa, sanyin jikinsa ya soma ragewa ssae,
Bayan ya kunna masa, ya fice daga ɗakin izuwa medication room ɗinsu, inda suke ajiyar magunguna,
Abunka ga professional surgeon doctor within minutes sai ga junaid yadawo cikin sense ɗinshi, bayan babban yayan nasu ya bashi medicine ɗinshi yasha,
Sannan yace “Bazan ƙyale ka Ba junaid, u must explain to me where did u go in this night, ka tanadi amsar da zaka bani before tomorrow, Kana mun wasa da lafiyarka ko?” sgr ya faɗi yana kallonsa A yayin da suke daga zaune saman gadon,’
narai narai junaid yayi da ido yana kallonsa, aiko hakan ya fusata sgr rai a6ace yace “zaka kwanta kayi bacci ko saina murƙusaka a wurin nan”? Koma wa junaid yayi tare da jan bargo ya lullu6e hada fuskarshi duka, bawan Allah yana so yace ma Babban yayan nasu Yunwa yake ji, amma ya gaza saboda ganin yadda ya fusata dashi,
Kwanciya shima sgr ɗin yayi yaja bargon ya lulu6e jikinsa har wurin neck ɗinsa sannan bacci ya kwashe su, su duka,
(Bacci da Yunwa😥)
________________________________________________________________
A 6angaren su hosana kuwa, tun da suka shiga cikin wannan tsohon store ɗin da Aunty babba ta turasu, Sam sun gaza samun sukuni, daker numfashin su ke fita saboda ƙura ga ko ina a tsohe ba windows,
Sun jima a tsaye cikin tashin hankali ga wani yin bacci da suke ji,
Jiki a mace hosana tace “nidae bacci nake ji, zan kwanta ko,a ƙasan ne,” ta faɗi tare da tattarewa zata kwanta ƙasa, ruƙo hannunta jahad tayi tare da cewa “A’a hosana in ki ka kwanta ƙasan nan wlh ƙwarin nan shigar miki cikin kunne zasuyi suyi miki illah,’ ta faɗi tana kallonta cikin karayar zuciya,
Muryar tamkar zatayi kuka hosana tace “to ya kike so nayi jahad ! A tsaye zamuyi baccin ne !!,
Jahad tace “a’a bari ki ga dabaran da zanyi mana mu kwanta,” tayi maganar tare da sakin hannun hosana ta wuce inda jarkokin nan suke burjiki, tasa hannu tashiga ɗauko su tana kwantar dasu ƙasa a jere, kusan jarka Goma sha biyu ne, ta rabasu shida shida biyu na jikin biyu su ka ɗanyi faɗi, sannan ta ta ɗauki tsumman dake a ƙasan ledar ɗakin tashiga kakka6esu saboda sunyi ƙura ssae ga matattun girgizo asaman su, daker tasamu suka ɗanyi haske sannan ta wurgar da tsumman, ta cire mayafin jikinta wanda saude tabata, ta shimfiɗa musu asaman jarkokin,
murmushi hosana tayi na jin daɗi ganin irin dabarar jahad, gashi ta mayar da Jarkoki sun zama kamar single bed,
Itama jahad ɗin murmushi tasaki tare da juyawa ta kalli hosana tace “To ya kika gani yanzu?
“Yayi kyau ssae jahad ,” ta bata amsa da murna a fuskarta,
“Zoki kwanta to,” jahad ta faɗi tana Yi mata alamar tazo ta kwanta,
Wuce wa hosana tayi tare da hayewa saman jarkokin ta kwanta, sannan itama jahad ta hau a hankali ta kwanta suna fuskantar junan su,
tace “mu kuma haka rayuwarmu zata ƙare Ko jahad? ko munyi addu’a Allah baya kar6a……
Cikin sauri jahad tace “Waya faɗa miki? Karna sake jin kince haka, Allah shi ya halicce mu, kuma yana sane damu, yana jarabtarmu ne ba don baya sonmu, face donya jaraba ƙarfin imanin mu, in har muka cinye jarabawar nan, zamu kasance masu nasara arayuwa,’
Hosana tace “Yaushe jarabawar zata ƙare jahad? Ae anyi mana dayawa yakamata suma wasu a ɗandana musu jarabawar mukuma mu huta,’
Murmushin takaici jahad tayi kafin tace “Allah shine mafi sani hosana, mu ci gaba da addu’a kawai kada mu daina, domin Allah yana fushi da duk wanda baya rokonsa,’
Cikin sanyin murya hosana tace “Insha Allah bazamu fasa Yin addu’a ba, muna kai kukan mu wurin Allah ba, har sai ranar da muka koma gare sa,
Murmushi jahad tayi tare da cewa “Hakane hosana,”
A haka har wani wahalallan bacci ya kwashe su, tsakar dare wani uban zafi ya fargar dasu, wata irin zufa ce ke zazzafowa daga jikinsu,
Hosana duk ta razana sai kuka take ta faman yi saboda bata da juriya duba da halin da take ciki ga ciwo ga ta6in hankali,
Daker jahad ta shawo kanta, da cewa ta kwanta ita zatayi mata fifita, cikin kuka tace “dame zakiyimun fifitar,”?
Jahad tace “Hijab ɗin jikin ki, zaki bani,” hannu hosana tasanya ta cire guntun hijab ɗin dake ajikinta wanda saude tabata, ta miƙawa jahad, Sannan ta kwanta saman jarkokin,
A haka Jahad ta shiga yi ma hosana fifita tana kore mata saurayen dake shawagi asama, nan take bacci ya ɗauki Hosana mai nauyin gaske,
Baiwar Allah Jahad idonta sunyi jawur saboda jin bacci, amma sam tagaza runtsawa saboda fifitar da take yima Hosana, tana tsananin tausayinta ssae, tana jin son ƴar uwarta bazata so wani abu ya kuma cutar da ita ba,
Tana Hamma tana yi mata fifita idonta na rurrufewa saboda bacci Amma haka ta jure ta tsayar da kanta don hosana tasamu isasshen bacci 😥 wani sa’in in tana gyangyaɗi har kusan faɗama Hosana take ta galabaita ssae,
Rayuwa kenan wasu mutanen basu da ɗigon imani aransu, basa tuna dame aka haliccesu, basa tuna ta yadda suka zo duniya, Son zuciya kawai, Ynx duk girman gidan general ishaq a ƙalla ba’a rasa bedrooms sama da shida, ga palor Amma a rasa inda za’a ba rai ya kwanta don baƙar mugunta da zalunci sai Store ɗin ajiye tarkacen buhunhuna da jarkoki? Wasu mutanen dae ba tausayi aransu,😿
Masu gidan na can suna shan ra6ar a.c a haɗaɗɗun bedrooms ɗinsu yayin da sukuma suke nan suna fama da Uban zafi, haƙiƙa su hosana sunyi dana sanin zuwansu gidan nan , sai suka ji dama Yaya Omar ya barsu gidan Goggon katsina da aunty saude, Allah sarki ƙaddara ta riga fata 😖
_ku gyara zama domin kuwa yanzu hot pages suka fara, da zafi zafinsu hada hayaƙi ma🔥😅 sannan na kashe part 3 duk yawan littafin zai ƙare a part 2 ne,
daga inda pages suka kai 100, zamu shiga part 2 Insha Allah, maganar payment kuma sam banaso nadaina posting a wannan grp ɗin, amma zan tafi hutu na shirya cigaban labari, a wannan time ɗin duk masu so zasu biya, sai aci gaba da sanya muku shi, ku haɗa kanku kawai ba dole sai kowa ya biya ba masu halin biya,iya adadin da suka biya zan fidda date na cigaba da posting ɗin shi, Just calm down ur mind anatare 💞👍
A posting ɗin yau maiya burgeku, mai kuma ya baku tausayi ? Mai kuma ya6ata muku rai? Sannan Idan Har kina da ƴar Uwa mai sonki kamar Jahad dan Allah kiyi mentioning ɗinta in ganta zanyi liking na Love ko Care

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Explore More

Download Complete Labarina Season 4 Episode 12 Kaɗan daga cikin shirin Hausa Novel PDF

February 14, 2024 0 Comments 0 tags

Haƙiƙa mutane da dama sun zaƙu kuma sun ƙagu suga abinda zai faru a cikin shirin Labarina abubuwa biyu ne zuwa uku ne mutane suke son a cikin shirin: Na

Download Complete Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 118 Hausa Novel PDF

February 14, 2024 0 Comments 0 tags

Father of soldiers TAKUN ƘARSHE Tashin hankalin da ba’a sa mashi date,Wani irin kallo Sgr ke bin Uncle abusufyan dashi,just speechless,Ya ƙame a tsaye ya kasa motsa lips ɗinsa,Sam ya

Download Complete Matar Damisa Book 1 Chapter 2 Hausa Novel PDF

February 14, 2024 0 Comments 0 tags

MALLAKIN Asmeetah *NASARA WRITERS ASSOCIATION* ___________________________________ {{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }} ___________________________________ https://www.facebook.com/103637491942644/ بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم Book One PAGES 11